Football

ALLAHU AKBAR: Tsohon Dan Wasan Kwallon Kafa ya Kar’bi Addinin Musulunci Yanzu a…

ALLAHU AKBAR: Tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ya karɓi Addinin Musulunci.

Tsohon ɗan wasan Spain Jose Ignacio Peleteiro wanda akafi sani da (Jota) ya karɓi Addinin Musulunci, Shine ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo kamar yadda jaridar Kuwait Daily Al Qabas ta rahoto a ranar Juma’ar da ta gabata.

Peleterio mai shekaru 32, Ya bayyana cewar ya karɓi Musulunci ne ganin yadda Iyalan abokin sa tsohon ɗan wasan ƙasar Kuwait Faisal Buresli suke tafiyar da al’amuran su a cikin addinin na Islama.

“Babu wani sarki sai Allah, Annabi Muhammadu Manzon sa ne. Nayi matuƙar farin ciki kuma na samu ƙarfi da na zama Musulmi, Wannan shine abu mafi muhimmanci a rayuwa ta.” Haka ɗan wasan ya faɗa lokacin da yake karɓar kalmar Shahada.

Bugu da ƙari ɗan wasan ya buga wasa a ƙungiyar rainon matasa ta Real Madrid Castilla, Celta Vigo, Eiber da Alavés lokacin yana Spain. Ya fafata wasa a Brentford, Birmingham City da Aston Villa lokacin da yakoma England. Yayi Ritaya daga ƙwallon ƙafa a shekarar 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button